Posts

Baban Khairat

Image
Baban Khairat Yau fa waƙa za na raira , Har da baitoci na tsara , Har kalamai ma na jera , Ba tare da na tsaya ba. Za na waƙe jarumina , Hazuƙi kuma malamina , Mai karantarwa da rana , Da daren ma bai bari ba. Shi fa malam in ka gan shi , Za ka gane ya na da kishi , Ga shi ba ya gani na ƙyashi , Ni ban san shi da kauce ƙa'ida ba. M. Rufa'i mijin Na'ima , Mai ƙokari waje na nema , Mai faɗawa mata su nema , Har mazan ma bai bari ba. Malamin nan na hadisi , Wanda ke aiki da nassi , Mai bayani na hadisi , Bai zamo mai aikata wargi ba. Ni du'a'i nak ka yo wa , Ilimi yai yo daɗawa , Har da baiwa yai ƙarawa , Ba tare da sun tsaya ba. Ni anan ne zan tsayawa , Rabbana yai yo tsarewa , Juriya kuma yai ta sawa , Kar ya barka kai yo gazawa , ✍ Abubakar Ibrahim Umar           *(Abu-Sahlah)* ©25/01/2022