Baban Khairat
Yau fa waƙa za na raira,
Har da baitoci na tsara,
Har kalamai ma na jera,
Ba tare da na tsaya ba.
Za na waƙe jarumina,
Hazuƙi kuma malamina,
Mai karantarwa da rana,
Da daren ma bai bari ba.
Shi fa malam in ka gan shi,
Za ka gane ya na da kishi,
Ga shi ba ya gani na ƙyashi,
Ni ban san shi da kauce ƙa'ida ba.
M. Rufa'i mijin Na'ima,
Mai ƙokari waje na nema,
Mai faɗawa mata su nema,
Har mazan ma bai bari ba.
Malamin nan na hadisi,
Wanda ke aiki da nassi,
Mai bayani na hadisi,
Bai zamo mai aikata wargi ba.
Ni du'a'i nak ka yo wa,
Ilimi yai yo daɗawa,
Har da baiwa yai ƙarawa,
Ba tare da sun tsaya ba.
Ni anan ne zan tsayawa,
Rabbana yai yo tsarewa,
Juriya kuma yai ta sawa,
Kar ya barka kai yo gazawa,
✍ Abubakar Ibrahim Umar
*(Abu-Sahlah)*
©25/01/2022
Comments
Post a Comment